Ilimi Hasken Rayuwa

Google: Dakin Karatun Gama Duniya

Sauti 10:01

Google injinin bincike ne da wasu Amurkawa guda biyu waton Larry Page da Sargey Brin suka samar a yanar gizo wanda zai bai wa mai bincike damar lalubu wani abu a yanar gizo muddun abun da ake nema an saka shi a yanar gizon, kuma gurin Google shi ne tattara bayanan duniya waje daya domin amfanar al’ummar duniya.A shekarar 2004 ne injinin bincike na Google a yanar gizo ya sanar da cewa zai samar da kafataren dakin karatu na gama duniya a yanar gizo wanda zai bai wa al’ummar duniya damar cim ma littafan karatu na marubuta daga sassan kasashen duniya baki daya. Domin cim ma wannan manufar ne kamfanin injinin binciken na Google ya shiga neman kawance da manyan dakunan karatu na duniya da suka hada da dakin karatun Jami’ar Harvard, da Michigan da Jami’ar Stanford da Jami’ar Oxford da kuma babban dakin karatun Birnin New York domin samar da hurumin da al’ummar duniya zasu yi amfani da littafansu.Sai dai kamfanin na Google a yanzu haka yana fuskantar kalubale daga marubuta wadanda suke ganin wannan yunkurin wata hanya ce da zata haifar da matsala a gare su musamman matsalar satar fasaha.To akan wannan batu dai shirin Ilimi Hasken rayuwa ya tattauna da Farfesa Abdalla Uba Adamu Marubuci kuma Masani a harkar ilimin fasahar sadarwa a Jami’ar Bayero a kano.