Ilimi Hasken Rayuwa

Shirin akan Dandalin zumunta na Twitter

Sauti 10:13

Twitter dandali ne na abokantaka da sada zumunci da ake amfani da shi ta intanet wanda ke sada mutum da mutane daga sassan kasashen duniya, kuma ana amfani da dandalin Twitter domin karba da tura sakwanni tare da wanzar da muhawara. Dandalin Twitter wasu Amurkawa ne guda uku suka samar da shi a San Fransisco kasar Amurka wato Jack Dosey da Evans Williams da kuma Biz Stone. Kuma an kaddamar da Twitter a shekarar 2006, tun lokacin ne kuma shafin Twitter ya samu karbuwa a kasashen Turai. An kiyasta cewa sama da mutane miliyan 200 ne ke amfani da dandalin na Twitter a duniya, sai dai kuma a kasashen Africa ba kasafai ake amfani da Twitter ba kamar Shafin dandalin Facebook. Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya yi nazari dangane da yadda ake amfani da Shafin dandalin Twitter tare da bayani akan muhimmancinsa.