Ilimi Hasken Rayuwa

Matsalolin Dake Tattare Da Jam'iar Karatu kai Tsaye Daga Gida

Sauti 10:00
RFI Hausa

Masu sauararen gidan Radio Faransa, barkan mu da saduwa a cikin shirin ilimi hasken rayuwa. A cikiin shirin za mu kawo muku irin kalubalen da ke gaban jami'ar yin karatu kai tsaye a gida , wato National Open University. Saboda jin karin haske na tuntubi wani malami a Jami'ar Jos, Mr. Solomon Dalung, shin mai zai ce dangane da batun jami'a karatu kai tsaye daga gida? A inda ya yi bayani game da irin kalubale da ke gaban jami'ar da kuma bayyana hanyoyin da za'a bi domin samun mafita.Na kuma ziyarci cibiyar jami'ar yin karatu kai tsaye da ke Jos babban birnin Jihar Filato a Najeriya a inda na zanta da manajan jami'ar Farfesa Isaac Butwat, dalilin kafa irin wannan jami'ar, a inda ya yi cikakken bayani dalilin kafa ta.Na kuma zanta da wasu dalibai da suka samu gurbin karatu a jami'ar a inda suka bayyana dalilin shigar su.