Ebola

WHO tace zanzu kam an sami rigakafin cutar Ebola

Wani jami'in kula da lafiya, yana bincike kan cutar Ebola
Wani jami'in kula da lafiya, yana bincike kan cutar Ebola RFI/Sébastien Nemeth

An tabbatar da sahihancin wani maganin rigakafin cutar Ebola mai saurin yaduwa, inda hukumar lafiya ta duniya WHO, data amince da aiki dashi tace yana aiki kashi 100 bisa 100, kimanin mako guda bayan amfani dashi.Cikin rahoton data fitar kan gwajin maganin, hukumar ta WHO tace sahihancin maganin, mai suna VSV-ZEBOV, wani mataki ne na kawar da cutar gaba daya.  

Talla

Yayin gwajin karo na farko, an sanyawa mutane da cutar tayi sanadiyyar mutuwar ‘yan uwansu, su 4,123 kwayoyin cutar, amma kuma basu nuna alamaun kamuwa da ita ba.
Al lokacin bincike na 2 kuma, an yiwa wasu mutanen su 3,528 allurar kwayoyin cutar ta Ebola, makonni 3 bayan sunyi mu’amala da wadanda ke fama da ita, amma 6 daga ciki ne kawai suka nuna alamun sun harbu.
Da wannan ne hukumar ta WHO tace yanzu kam, an samu magani abin dogaro wajen yaki da cutar ta Ebola.
Mutane dubu 28 ne suka kamu da cutar data barke a baya bayan nan cikin kasashen Guinea, Liberia da Saliyo, wadda kuma tayi sanadiyyar rasa ran mutane dubu 11.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI