lafiya

Masu kiba na samun karancin rayuwa a duniya

Masana kiwon lafiya sun ce kibar da ta wuce kima na haddasa cututtuka da dama
Masana kiwon lafiya sun ce kibar da ta wuce kima na haddasa cututtuka da dama REUTERS/Finbarr O'Reilly/Files

Wani binciken masana kiwon lafiya ya nuna cewar mutanen da ke da kibar da ta wuce kima na fuskantar barazanar raguwar shakara guda zuwa 10 daga cikin shekarun da za su yi a rayuwa.

Talla

Binciken wanda ya bambamta da wanda aka yi a baya da ya nuna babu wata damuwa game da samun kibar ya ce, masu irin wannan kibar da ta wuce kimar na iya mutuwa kafin cika shekaru 70.

Babbar jami’ar da ta jagoranci binciken a Jami’ar Cambridge, Emanuele Di Angelantonio ta ce kibar na haifar da cututuka da suka kunshi ciwon zuciya da shanyewar wani bangare na jiki da matsalar numfashi da kuma cutar kansa.

An dai gudanar da binciken ne kan mutane miliyan 4 a nahiyoyi 4 na duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.