HIV-AIDS

An samu sakamako mai karfafa gwiwa a gwajin rigakafin Sida

Samfurin Kwayoyin rigakafin Sida
Samfurin Kwayoyin rigakafin Sida AFP PHOTO / ADEK BERRY

An samu sakamako mai karfafa gwiwa a kokarin da ake na samar da rigakafin cutar HIV ko Sida mai karya garkuwar jiki, kamar yadda masu bincike suka sanar a taron kasa da kasa da ake gudanarwa kan Sida a Durban na Afrika ta kudu.

Talla

Bayan shafe tsawon watanni 18 ana kokarin gwajin rigakafin samfurin HVTN100 domin tabbatar da ingancin sa, taron dake samu halartar mutane 252 ya gamsu da sakamakon.

Cutar Sida ta fi ta’addi a Afrika ta Kudu dake karban bakawanci wanann taro, inda ta lakume rayuka sama da miliyan 30 cikin shekaru sama da 30 da suka gabata.

Taron a yanzu ya amince da a fara gwajin Rigakafin amma ta hanyoyi Uku, da kuma duba matakan da za a bi, da kuma tabbatuwar inganci rigakafin.

Jagorar Binciken, Kathy Mngadi tace za a gudanar da gwajin domin gani ko garkuwan jiki zai iya daukan wannan rigkafin ba tare da haifar da wata illa ta daban ba, maimakon a warke baki daya.

Kathy ta ce a watan Nuwamba zasu sake gudanar da kwajin rigakafi na biyu, samfurin HVTN702 kan mutane sama da dubu 5 mata da maza ‘yan asalin Afrika ta kudu da shekarunsu ya kama daga 18-25.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.