lafiya

Za a haifi dubban jarirai da nakasa saboda Zika

Cutar Zika na haddasa haihuwar yara da nakasa musamman a kawunansu
Cutar Zika na haddasa haihuwar yara da nakasa musamman a kawunansu REUTERS/Ueslei Marcelino

Akwai yiyuwar za a haifi dubban jarirai dauke da nakasa sakamakon kamuwa da cutar Zika, kamar dai yadda rahoton wani bincike na baya-bayan nan ya nuna.

Talla

Rahoton ya ce matsalar za ta fi shafar kasashen yankin Latin Amurka da kuma Caribbean  inda mata milyan daya da dubu 650 da ke dauke da juna biyu, ke iya kamuwa da cutar ta zika a wadannan kasashe.

Binciken ya ce ko shakka babu, dubbai daga cikin wadannan mata za su iya kamuwa da cutar, sannan kuma ta kasance dalilin haifar yara da ke dauke da nakasa musamman a kawunansu.
 

A jumulce dai an kiyasata cewa akwai mutane kusan milyan 90 a yankin na Latin Amurka da Caribbean da aka tabbatar da cewa suna dauke da cutar ta Zika wadda ta fara bayyana a cikin shekarar da ta gabata.

Masu binciken sun ce abu ne mai yiyuwa adadin ya kere haka, domin akwai wasu da ke dauke da cutar amma an kasa fahintar hakan.

A kasar Brazil kawai akwai masu dauke da cutar sama da milyan 14, yayin da kasashen Mexico da kuma Venzuela ke biye ma ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.