Zama kusa da tittuna na haddasa mantuwa
Wallafawa ranar:
Wani bincike masana kiwon lafiya daga Britaniya, ya ce zama kusa da manyan tittuna na haddasa ciwon mantuwa.Masanan sun tabbatar da haka ne bayan aiwatar da kwaje-kwaje kan wasu mutane miliyan 6 tsakanin 2001-2012.
Binciken da aka wallafa a jaridar kiwon lafiyar Britaniya, na cewa mutane da ke zaman tazarar mita 50 da tittuna da ake hada-hada su sukafi kamuwa da kashi 7 cikin 100 na ciwon mantuwa.
Binciken da aka aiwatar kan rayuwar mutum miliyan 6 a Kanada tsawon shekara 11, sun ce gurbatacciyar iska da hayaniyar ababen hawa na tasiri ga dakushewar kwakwalwa.
A cewar Hukumar lafiya ta WHO, mutane miliyan 47 da rabi ke fama da ciwon mantuwa a duniya, wanda ke tasiri matuka ga rayuwar su.
Kuma a kowacce shekarar a kan samu mutane sama da miliyan 7 dauke da ciwon na mantuwa inda kashi 60 zuwa 70 daga cikinsu kan kare rayuwarsu cikin karkarwar jiki.
Ciwon mantuwa na hadda shanyewan jiki da hawan jinni a cewar masana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu