Lafiya Jari ce

Littafin Hausa da ke magana kan yanayin ciki da haihuwa

Sauti 10:05
Mace dauke da juna biyu
Mace dauke da juna biyu Reuters

Najeriya kasa ce da ake fuskantar yawan mutuwar mata a lokacin da suke dauke da juna biyu ko kuma a lokacin haihuhuwa, lamarin da ya sa masana kiwon lafiya ke ci gaba da yin kira domin wayar da kan dangane da yadda za a ceto rayuwar mata da ma kananan yara.Daya daga cikin matakan da aka fara dauka sun hada da wallafa littafi da ke kunshe da bayanai dangane da kiwon lafiyar mace daga lokacin da ta dauki ciki har zuwa haihuwa a cikin harshen Hausa.A shirin na wannan karo, Umaymah Sani Abdulmumin ta mayar da hankali ne dangane da wannan batu.