Lafiya

Ana samun jan kafa wajen magance Malaria-WHO

Cutar Malaria na ci gaba da kashe mutane musamman a kasashen Afrika
Cutar Malaria na ci gaba da kashe mutane musamman a kasashen Afrika Adam M. Richman / Sanaria Inc. / AFP

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar, ana fuskantar matsaloli sosai wajen shawo kan yaduwar cutar zazzabin cizon sauro, wanda ke ci gaba da hallaka rayuwa a kasashe da dama.

Talla

Rahoton hukumar ya ce a shekarar 2016 an samu karuwar wadanda suka gamu da cutar sama da miliyan 5 sabanin na shekarar 2015, yayin da adadin mutanen da suka rasu ya kai 445,000 sabanin 446,000 a shekarar da ta gabata.

Darakta Janar na hukumar, Dr. Tedros Adhanom Ghebreysus ya ce, yanzu haka suna fuskantar mawuyacin hali, kuma rashin daukar mataki ka iya mayar da hannun agogo baya kan shirin magance cutar nan da shekarar 2020.

Daraktan ya ce a shekarar da ta gabata, an kashe sama da Dala biliyan biyu da rabi wajen tinkarar cutar, duk da cewa ana bukatar Dala biliyan 6 da rabi ne don magance  cutar.

Daraktan ya bayyana kasashen Afrika a matsayin kashi 90 cikin 100 na masu fama da cutar, yayin da hukumar ke taimakawa wajen magance cutar a kasashen Najeriya da Sudan ta Kudu da Venezuela da Bolivia da kuma Yemeno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.