Lafiya

Mata masu ciwon zuciya ka iya mutuwa idan likita namiji ke kula da su

Bincike ya nuna Mata masu fama da cutar zuciya ka iya mutuwa da wuri idan likitansu namiji ne.
Bincike ya nuna Mata masu fama da cutar zuciya ka iya mutuwa da wuri idan likitansu namiji ne. Medical Xpress

Wani binciken masana kiwon lafiya a Amurka kan matan dake dauke da cutar bugun zuciya ya nuna cewar matan dake gobe da nisa sakamakon cutar na iya mutuwa idan likitan dake kula da su namiji ne, maimakon mace.

Talla

Binciken ya biyo bayan gwajin da akayi kan masu fama da cutar 500,000 da aka ruga da su dakin kwanciyar marasa lafiya na gagagwa saboda gamuwa da bugun zuciyar tsakanin shekarar 1991 zuwa 2010.

Binciken da masana kiwon lafiya daga Jami’ar Havard suka gudanar sun gano cewar likitoci mata sun fi kula da marasa lafiyar fiye da takwarorin su maza.

Rahotan yace kasha 12 na marasa lafiyar da aka ruga da su asibiti sakamakon bugun zuciya sukan mutu a Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.