Kwalara ta kashe mutane 500 a tafkin Chadi
Majalisar Dinkin Duniya ta ce, tun farkon wannan shekara ta 2018, sama da mutane 500 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar annubar amai da gudawa wato Kwalara a kasashen da ke yankin Tafkin Chadi.
Wallafawa ranar:
A wani rahoto da ta fitar a ranar Laraba, Hukumar Ayyukan Jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana alkaluman da ke cewa, sama da mutane dubu 27 ne suka kamu da cutar a yayin da 510 daga cikinsu suka rasa rayukansu a cikin makwanni 35 a kasashen na yankin Tafkin Chadi, sakamakon da ya rubanya har sau 10 idan aka auna da wanda aka samu a shekaru 4 da suka gabata.
Hukumar Lafiyar ta yi gargadin cewa, idan har ba a gaggauta daukar mataki ba to lamarin na iya kazancewa wanda zai iya kai ga mutane miliyan 6 da anobar za ta shafa.
Yankin Tafkin Chadi ya hada kasashen Tarayyar Najeriya da Kamaru da Chadi da kuma Jamhuriyar Nijar, kasashen da kuma ke fama da tashe- tashen hankullan 'yan tsageran Boko Haram
Hukumar Ayyukan Jinkan ta ce, a Nigeriya ne lamarin yafi yin kamari, in da mutane dubu 24 suka kamu, al’amarin da hukumar ta ce, akwai bukatar gaggauta daukar matakai domin dakatar da ci gaban yaduwar annubar cikin gaggawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu