Lafiya

Shakar gurbatacciyar iska na haifar da cutar mantuwa

Wani sabon binciken masana lafiya ya gano cewa gurbatacciyar iskar da mutane ke shaka na haifar da cutar yawan mantuwa da wasu ke fama da ita.

Wani sakamakon binciken masana ya nuna cewa, rashin jin kamshi ko wari ga mutum, ka iya zama daya daga cikin alamun shirin kamuwa da cutar mantuwa
Wani sakamakon binciken masana ya nuna cewa, rashin jin kamshi ko wari ga mutum, ka iya zama daya daga cikin alamun shirin kamuwa da cutar mantuwa The Independent
Talla

Rahoton wanda aka wallafa a yau Laraba ya kara da cewa, yawan shan barasa, taba sigari da makamantansu basu kai gurbatacciyar iska da mutane ke shaka hadari wajen haddasawa mutane cutar yawan mantuwa ba, wato dementia.

Masanan da suka gudanar da wannan bincike sun fito ne daga manyan kwalejojin kimiyya da kuma jami’ar birnin London.

Kwararrun sun gudanar da binciken ne ta hanyar bibiyar wasu mutane dubu 131,000 wadanda shekarunsu ke tsakanin 50 zuwa 79.

Masanan sun yi ta bibiyar lafiyar baki dayan mutanen har tsawon shekaru 7 daga shekarar 2004 zuwa 2013.

A tsakanin 2005 zuwa 2013 ne masanan suka gano cewa mutane 2,181, sun kamu da cutar mantuwa ta dementia, kuma dalilin kamuwarsu da cutar shi ne shakar gurbataciyyar iska mai kunshe da sinadarin nitrogen dioxide, kamar yadda binciken da suka gudanar a gaf da gidajen marasa lafiyar ya tabbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI