Lafiya Jari ce

Cutar Malaria na kamari a lokacin damina

Sauti 09:22
Cutar Malaria ta fi kama mata masu juna biyu in ji kwararrun kiwon lafiya
Cutar Malaria ta fi kama mata masu juna biyu in ji kwararrun kiwon lafiya REUTERS/James Gathany

Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon tare da Azima Bashir ya tattauna ne game da cutar Zazzabin Cizon Sauro ko kuma Malaria a lokacin damina da kuma matakan kare kai daga kamuwa da cutar. Likitoci sun ce, cutar ta fi yaduwa a irin lokacin na damina.