Bakonmu a Yau

Ahmad Yakasai na kungiyar masana hada magunguna kan zargin ana hada wasu magungunan China da sassan jikin Dan Adam

Sauti 03:26
Ana zargin akwai magungunan da ake shiga Najeriya da su daga China, wadanda aka hada da sassan jikin Dan Adam.
Ana zargin akwai magungunan da ake shiga Najeriya da su daga China, wadanda aka hada da sassan jikin Dan Adam. Reuters/Thomas Mukoya

Hukumomin Najeriya sun kaddamar da bincike domin gano wasu magunguna da ake zargin cewar ana hada su a kasar China da sassan jikin Bil Adama da suka hada da mahaifa.Tuni gwamnatin ta baiwa hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta NAFDAC da jami’an kwastam umurnin cewar basu bari an shigo da magungunan Najeriya ba.Akan wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban kungiyar masana hada magunguna a Najeriya, Pharm Ahmed Yakasai kuma ga yadda zatawar su ta gudana.