Lafiya

Karnuka na iya gano cutukan dake damun dan Adam - Masana

Freya, daya daga cikin karnukan da masana suka horar wajen gano mai dauke da cutar Malaria kafin ta kai ga bayyana.
Freya, daya daga cikin karnukan da masana suka horar wajen gano mai dauke da cutar Malaria kafin ta kai ga bayyana. Medical Xpress

Masana Kimiya sun bayyana cewar ana iya horar da karnuka domin gano wasu nau'ukan cutar kansa da masu fama da cutar hawan jinni da kuma cutar zazzabin sauro a kananan yara wajen sinsina safar da suke sanye da ita.

Talla

Binciken wanda aka wallafa a Mujallar masana magunguna dake Amurka, a taron dake gudana a New Orleans, yace an horar da irin wadanan karnuka domin gano cutar daga yara a Afirka wadanda basu ma fara nuna alamara kamuwa da ita ba.

James Logan, jami’in da ya jagoranci binciken daga makarantar kula da cututtukan da ake samu a Yankunan Sahara da ake kira London School of Hygiene and Tropical Medicine, yace ganin yadda kokarin samun cigaba wajen yaki da cutar malaria ya kasa samun nasara, ya dace a samo sabbin dabarun zamani.

Logan yace daga cikin safa 175 da karnukan suka sinsina, an gano 30 da suke dauke da cutar malaria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.