Lafiya

Ana bukatar shekara akalla 1 wajen samun tazarar haihuwa - Masana

Bayar da tazarar daukar juna biyu ta akalla tsawon watanni 12 yana rage yawan hadarin da mai ciki ke fuskanta.
Bayar da tazarar daukar juna biyu ta akalla tsawon watanni 12 yana rage yawan hadarin da mai ciki ke fuskanta. AFP/File

Masana kiwon lafiya sun baiwa matan dake tsakanin shekara 30 zuwa 40 dake bukatar daukar juna biyu shawara kan tazarar da ya dace a samu domin kare lafiyar su.

Talla

Rahotan wani bincike da masanan suka yi wanda aka wallafa shi a Mujallar kula da lafiya ta Amurka tace ana bukatar akalla shekara guda ko kuma biyu wajen daukar cikin, duk da yake daukar juna biyu ga masu shekarun da suke da yawa na tattare da hadura.

Laura Schummers ta Jami’ar British Columbia dake Amurka da ta jagoranci binciken da aka gudanar, tace binciken ya nuna hadari wajen daukar ciki ga matan da suka wuce shekaru 35, sabanin masu kasa da wadanan shekarun.

A kasar Amurka likitoci kan baiwa mata shawarar samun tazarar akalla watanni 18 kafin sake samun ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.