Lafiya

Mutum na 2 ya warke daga cuta mai karya garkuwar jiki

A karo na 2 cikin tsawon shekaru sama da 20 bayan bullar cuta mai karya garkuwar jiki ta AIDS, an samu mai dauke da kwayar cutar ta HIV da a yanzu ya warke sarai.

Mutum na 2 da ke dauke da kwayar cutar HIV ya warke.
Mutum na 2 da ke dauke da kwayar cutar HIV ya warke. Reuters TV
Talla

Mutumin da ya kafa tarihin dai mazaunin birnin London ne wanda likitoci suka tabbatar da warkewarsa bayan gwajin tsawon watanni 19.

A watan Yuni na shekarar 1981, likitoci a Amurka suka soma gano wasu mutane biyar masu auren jinsi guda da suka kamu da cutar AIDS a jihar California, bayan da suka kamu da nau’in zazzabin numonia mai zafi.

Sai dai ba’a kai ga radawa cuta mai karya garkuwar jikin suna ba, sai a shekarar 1982, a 1983 kuma aka radawa kwayar cutar da ke haifar da AIDS sunan HIV.

A watan Maris na shekarar 1987 aka soma amfani da maganin rage kaifin cutar AZT a Amurka, daga bisani hukumar lafiya ta Duniya WHO ta bayyana 1 ga Disamba na 1988 a matsayin ranar bikin wayar da kan jama’a kan cutar mai karya garkuwar jiki.

A watan Nuwamban 1999, wani rahoton hadin gwiwar hukumar lafiya ta duniya WHO da Majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa yawan mutanen da suka kamu da kwayar cuta mai karya garkuwar jiki a duniya, tun bayan bullarta ya zarta miliyan 50, miliyan 16 daga ciki kuma suka hallaka a dalilin cutar.

A watan Fabarairu na 2003, shugaban Amurka George W. Bush ya kaddamar da shirin gaggawa na shawo kan barnar da cutar AIDS ke yi a duniya, musamman a nahiyar Afrika da kuma yankin Carribean.

A karon farko wajen soma aiwatar da shirin, gwamnatin Bush ta bayar da tallafin dala biliyan 15.

Zuwa shekarar 2018 kuwa, asusun bada tallafin yakar cuta mai karya garkuwar jikin PEPFAR ya samar da tallafin dala niliyan 70.

A shekarar 2009, aka fara samun mara lafiya na farko mai suna Timothy Brown da ya warke daga cutar AIDS a Berlin babban birnin Jamus, sai kuma mutum na 2 da ya warke daga cutar a shekarar 2019 da muke ciki dake birnin London.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI