An kaddamar da shirin baiwa marasa lafiya gudunmawar jini a Najeriya

Sauti 10:03
Masana lafiya da sauran masu ruwa da tsaki, sun soma kokarin saukaka baiwa marasa lafiya gudunmawar jini a tarayyar Najeriya.
Masana lafiya da sauran masu ruwa da tsaki, sun soma kokarin saukaka baiwa marasa lafiya gudunmawar jini a tarayyar Najeriya. Reuters

Shirin Lafiya Jari Ce na wannan mako, yayi tattaki zuwa babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, inda aka kaddamar da wani shirin bada gudunmawar jini ga marasa lafiya, saboda karancinsa ko tsada da ake fuskanta a sassan Najeriya, matsalar da tafi shafar talakawa marasa karfi.