An samu karuwar masu kamuwa da cutar Kyanda a duniya- WHO
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO, ta ce yaduwar cutar kyanda a duniya ta karu da ninki hudu a watanni uku na farkon wannan shekara, idan aka kwatanta da bara, in da ta nuna damuwa kan tasirin maganin riga-kafin cutar.
A cewar Hukumar Lafiyar, Cutar mai saurin yaduwa, ana iya kiyaye kwayoyin cutar, ta hanyar amfani da maganin allurar riga-kafi guda biyu kachal bisa al’ada, to amma sai ga shi tana taba kasashe da dama a fadin duniya, sakamakon rashi ko rashin bin ka’idojin anfani da allurar riga-kafin.
Hukumar ta ce, bazuwar cutar ta ninka har sau hudu, a watanni uku na farkon shekara, idan aka kwanta da yadda take a bara a dai-dai wannan lokaci, inda tace lamarin ya fi kamari a nahiyar Afirka, inda cutar ta ninka sau 7, nahiyar Turai ke biye mata da ninki 3, sai yankin Gabashin tekun Bahrurum da ninki daya.
A nahiyar Amurka ma cutar ta karu ta kashi 60 cikin dari, sai kuma kasashen Asia da Pacific, in da ta karu da kashi 40 cikin dari, idan aka kwatanta da bara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu