Isa ga babban shafi
Lafiya

Kisan jami'an lafiya na dakile yunkurin kawar da manyan cutuka - Rahoto

Wasu jami'an lafiya a garin Butembo a Jamhuriyar Congo da ke lura da masu dauke da cutar Ebola. 28/3/2019.
Wasu jami'an lafiya a garin Butembo a Jamhuriyar Congo da ke lura da masu dauke da cutar Ebola. 28/3/2019. REUTERS/Baz Ratner
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman | Azima Bashir Aminu
Minti 2

Sakamakon wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa hare-hare kan jami’an kiwon lafiya, suna dakile yunkurin da ake yi na yaki da manyan cutuka a sassan duniya, ciki har da cutukan Polio da kuma Ebola galibi a kasashen Afrika da nahiyar Asiya.

Talla

Wata kungiya mai rajin tabbatar da isar da agajin magunguna zuwa yankunan da ke fuskantar rikici ta SHCC ce ta fitar sakamakon binciken a yau Laraba, inda ta ce adadin jami’an lafiyar da aka kashi a bara, ya haifar da tsaiko ga yunkurin da ake na agazawa masu fama da cutar Ebola da kuma dakile kokarin isar da magungunan rigakafin cutar Polio a wasu yankunan Asiya.

Kungiyar ta ce cikin shekarar da ta gabata, an kaddamar da hare-hare har sau 973 kan jami’an lafiya a kasashe daban-daban masu fuskantar rikici inda ta kai ga kisan jami’an 167, dai dai lokacin da su ke tsaka da aikinsu.

Zalika binciken kungiyar ya nuna cewa, jami’an lafiya 710 ne suka samu muggan raunuka a hare-haren bom ko mamayar asibitoci da ‘yan tawaye ke yi, garkuwa da su, ko kuma kaiwa motocin agaji farmaki da suke yawan yi.

Binciken ya nuna cewa hare-haren kan jami’an agaji ya karu a bara idan aka kwatanta da na shekarar 2017 inda aka kai musu farmaki har sau 701 a kasashe 23.

Kasashen da jami’an lafiyar suka fi fuskantar kalubale a cewar rahoton sun hada da Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, Pakistan, Somalia. Yayinda sauran kasashen suka kunshi, Syria, yankin Falasdinu da kuma Afghanistan, sai kuma Yemen, Libya da Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.