Isa ga babban shafi
Lafiya

Za a yi amfani da Dala miliyan 100 wajen magance cizon maciji

Wani Maciji kwance a ciyawa ya kanannade jikinsa
Wani Maciji kwance a ciyawa ya kanannade jikinsa Daily mail
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris
1 Minti

Wata Gidauniyar Lafiya ta Duniya ta sanar da shirin zuba sama da Dala miliyan 100 a asusun samo ingantaccen maganin cizon maciji wanda ke hallaka akalla mutane 120,000 kowacce shekara a fadin duniya.

Talla

Gidauniyar wadda ta ‘Wellcome Trust Global Health Charity’ an kaddamar da ita ne a birnin London da zummar samo ingantaccen maganin cizon maciji wanda ya fi wanda ake amfani da shi yanzu domin amfani da shi nan gaba.

Farfesa David Lallo, daraktan Cibiyar Yaki da Cututtukan da ake samu a yankin sahara da ke Liverpool, ya ce yanzu haka maganin yaki da cizon macijin da ake amfani da shi, magani ne da aka samu shekaru 100 da suka gabata.

Lallo ya ce, rashin kudaden gudanar da bincike, na yin illa ga nazarin kimiya musamman a bangaren kula da kafiya, abinda ke kai ga dubban mutane suna rasa rayukansu.

Philip Price, masani kan cizon maciji ya ce, macizai na hallaka mutane kusan 120,000 kowacce shekara a yankunan karkarar da ke Afrika da Asia da Kudancin Amurka, inda ya bayyana matsalar a matsayin wadda ba a cika mayar da hankali akai ba.

Masanin ya ce, wasu mutane 400,000 na samu raunuka daban daban da suke kai ga yanke kafarsu saboda saran maciji.

Ana saran Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar da wani shirin dakile mutuwa samakon cizon maciji nan da shekarar 2030 a wannan watan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.