Isa ga babban shafi
WHO-Lafiya

WHO ta samar da sabuwar dubarar rage illar cizon maciji

Hukumar lafiyar ta duniya WHO ta ce cizon majici na cikin jerin cutuka mafiya hadari a duniya
Hukumar lafiyar ta duniya WHO ta ce cizon majici na cikin jerin cutuka mafiya hadari a duniya google.com
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
2 Minti

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta kaddamar wata sabuwar dabarar dakile radadi da mutuwa da cizon macicji ke haddasawa, tana mai kashedin cewa karancin maganin dafin maciji na iya kasancewa annoba a fannin kiwon lafiyar al’umma.

Talla

Alkaluman Hukumar Lafiya ta WHO na nuna cewa, kusan mutane miliyan 3 macizai masu dafi ke cizon su duk shekara, kuma akalla mutane dubu 81 zuwa dubu 138 ke mutuwa sakamakon hakan, sai kuma karin wasu dubu 400 da kan sha da kyar wadanda hukumar ta ce kan yi fama da nakasa ta dindindin ko kuma shiga wani yanayi mara armashi.

A wani sabon rahoto, hukumar ta bukaci kasashen duniya da su dau matakan warware matsalar, ta na mai kashedin cewa har yanzu hukumomi da gwamnatoci ba sa daukar matsalar ta cizon majici a matsayin babban kalubalen lafiya.

Hukumar Lafiyar wadda ta sanya cizon macizai masu dafi cikin jerin cutuka da ake wa rikon sakainar kashi, ta gabatar da wata dabarar da za ta rage mace-mace da kuma nakasar da dafin maciji ke haddasawa.

Dafin maciji na iya haddasa mutuwar barin jiki da ke kawo daukewar numfashi, mummunar zubar jini da matsalar koda da ciwon jijiyoyi da ka iya kaiwa ga nakasa.

Akasarin wadanda ke gamuwa da wannan iftila’in na cizon maciji suna nahiyoyin da talauci ya yiwa kanta ne, kuma yara ne suka fi fuskantar matsalar.

Bangare mafi mahimmanci na wannan dabarar shine kara azama wajen samar da maganin dafin macicji mai inganci, wanda tun a cikin shekarun 1980s wasu kamfanoni suka yi watsi da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.