Isa ga babban shafi
Lafiya

An gano maganin da ake sa ran zai hana kamuwa da cutar Kanjamau

Wasu magungunan rage kaifin Cutar Sida.
Wasu magungunan rage kaifin Cutar Sida. TANG CHHIN Sothy / AFP
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman | Bashir Ibrahim Idris
Minti 1

Masana Kimiya sun samar da wani maganin da ake ganin zai iya hana mutane kamuwa da cutar sida ko kanjamau na shekara guda idan sun yi amfani da shi, kamar yadda bincike ya nuna.

Talla

Yayin gabatar da binciken da suka yi a Mexico, wajen taron masana cutar na 10 a Mexico, masanan sun bayayna ceawar maganin da aka samar mai kamar tsinke ashana, na iya zama wani gagarumin cigaba wajen rage kamuwa da cutar.

Darakta Janar na Cibiyar gudanar da binciken, Mike Robertson yace amfani da maganin zai taimaka wajen sanya wasu sinadaren da za su iya kare jama’a daga kamuwa da cutar.

Majalisar Dinkin Duniya tace an samu raguwar masu kamuwa da cutar zuwa kashi daya bisa uku daga shekarar 2017 zuwa 2018, adadin da ya kai 770,000 a fadin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.