Ebola

Bankin Duniya ya ware Dala miliyan 300 don yaki da Ebola

Cutar Ebola ta kashe mutane sama da dubu 1 da 700 daga watan Agustan bara a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo
Cutar Ebola ta kashe mutane sama da dubu 1 da 700 daga watan Agustan bara a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo REUTERS/Samuel Mambo

Bankin Duniya ya sanar da ware tallafin Dala miliyan 300 a matsayin agaji ga Jamhuriyar Dimokradiyar Congo domin kawar da cutar Ebola da ta sake barkewa a kasar.

Talla

Tallafin kudaden na zuwa ne bayan Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ayyana dokar ta baci a bangaren kiwon lafiyar Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo, lamarin da ta ce, akwai bukatar kasashen duniya su mayar da hankali akai.

Tallafin na baya-bayan nan zai kasance kari kan Dala miliyan 100 da Bankin Duniyar ya bayar a cikin watan Agustan shekarar 2018 domin magance cutar ta Ebola a kasar.

Shugabar Bankin Duniyar, Kristalina Georgieva ta ce, dole ne a dauki matakan gaggawa domin hana yaduwar cutar wadda ta lakume rayukan jama’a da dama a Jamhuriyar Congo.

Shugabar ta kara da cewa, akwai bukatar kasashen duniya su kara kaimi wajen agaza wa jami’an kiwon lafiya da ke aiki tukuru don ganin an samu nasarar kawar da cutar baki daya.

Tun a cikin watan Agustan shekarar bara, cutar ta kashe mutane sama da dubu 1 da 700 daga cikin jumullar mutane dubu 2 da 500 da cutar ta kama a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.