Lafiya

Masu cutar kyanda sun karu a duniya

Allurar rigakafin cutar Kyanda
Allurar rigakafin cutar Kyanda Reuters/Lindsey Wasson

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, an samu karuwar masu kamuwa da cutar kyanda a duniya har ninki uku a watanni bakwai na farkon wannan shekarar a daidai lokacin da hankula suka tashi ganin yadda wasu al’umomi ke nuna turjiya game da karbar rigakafinta.

Talla

Kawo yanzu an bada rahoton cewa, mutane sama da dubu 360 ne suka harbu da cutar kyanda a fadin duniya, idan aka kwatanta da shekararr 2018, inda mutane 129, 239 suka kamu da cutar.

Mai magana da yawun hukumar, Christian Lindmeier ya shaida wa manema labarai a birnin Geneva cewa, rabon a samu irin wannan adadi mai yawa tun shekarar 2006, yana mai cewa, abinda ya fi tada hankali game da wannan lamari shi ne, mutum daya cikin goma da suka harbu da cutar ne ake samun sukunin sanarwa a fadin duniya.

An samu karuwar kamuwa da cutar kyandar a duniya, inda nahiyar Afirka ta fi tsunduma cikin matsalar da karuwa har  kashi 900, yayinda ta karu a yankin yammacin Pacific da kashi 230.

A Amurka, mutane dubu daya da 164 suka kamu da cutar a wannan shekarar idan aka kwatanta da 372 a shekarar da ta gabata, adadi mafi yawa cikin shekaru 25, yayinda a yankin Turai aka samu mutane dubu 90 da cutar ta kama a wannan shekarar sabanin sama da dubu 84 a bara.

Kyanda dai cuta ce da ke sa zazzabi, tari da kuraje da ka iya zama sanadin mutuwa a wasu lokuta, kuma hukumar lafiya ta duniya ta ce, babu hadari a rigakafinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.