Isa ga babban shafi
Lafiya

Masu fama da ciwon Suga sun karu a duniya

Masu cutar Suga sun zarce miliyan 420 a duk fadin duniya a yanzu
Masu cutar Suga sun zarce miliyan 420 a duk fadin duniya a yanzu REUTERS/Mario Anzuoni
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Bashir Ibrahim Idris
1 Minti

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da wani shiri da zai rage farashin maganin insolin da masu fama da ciwon Suga ke bukata, a daidai lokacin da ake bikin ranar yaki da masu fama da cutar a wannan Alhamis.

Talla

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa kan karuwar mutanen da ke fama da cutar a fadin duniya, inda take cewa adadin ya ribanya har sau 3 daga yadda matsalar take shekaru 35 da suka gabata.

Hukumar ta ce, yanzu haka masu fama da cutar a duniya sun zarce miliyan 420 daga cikin miliyan 180 da ake da su a shekarar 1980, yayin da hukumar da ke kula da masu fama da cutar ta ce, adadin na iya kaiwa miliyan 629 nan da shekarar 2045.

Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, cutar na yaduwa sosai a duniya, kuma an fi samun ta a kasashen da ke da jama’a marasa karfi.

Hukumar ta bayyana cutar a matsayin ta 7 daga cikin manyan cututtukan da suka fi kisa a duniya, wanda ke haifar da cutar bugun-zuciya da shanyewar barin jiki da cutar koda da makanta da kuma yankewar hannaye da kafafuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.