Lafiya

Cutar Kyanda ta kashe mutane dubu 140

Masana kiwon lafiya sun ce, karbar allurar riga-kafi na taka rawa wajen magance cutar Kyanda a duniya.
Masana kiwon lafiya sun ce, karbar allurar riga-kafi na taka rawa wajen magance cutar Kyanda a duniya. AFP Photo/ASHRAF SHAZLY

Alkaluman Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da Cibiyar Nazari da Yakar Cutuka ta Amurka, sun bayyana cewa, sama da mutane dubu 140 suka mutu sakamakon cutar kyanda a shekarar 2018. Wannan na zuwa ne a yayin da cutar ta yi kamari a kasashen duniya.

Talla

An samu mafi yawan asarar rayukan ne a tsakanin yara ‘yan kasa da shekaru 5, yayin da bayanai nke cewa, a halin yanzu, kananan yara da suka hada da jarirai na fuskantar gagarumar barazanar kamuwa da cutar wadda kuma za ta iya haddasa kazancewar ciwon sanyin hakarkari da kumurar kwakwaluwa har da nakasa ta din-dindin baya ga makanta da kurmancewa.

Wasu hujjoji da aka wallafa a baya-bayan nan, sun nuna cewa, kwayar cutar Kyanda na wargaza garkuwar jikin dan adam na tsawon watanni ko kuma shekaru.

Har ila yau, rashin karsashin wannan garkuwa na tasiri wajen bude kofar kamuwa da wasu cutuka masu laukume rayuka da suka hada da matsananciyar mura da gudawa.

Darekta Janar na Hukumar Lafiya ta Duniya, Dr. Tedros Adhanom Ghebreysusu, ya ce, abin takaici ne yadda kananan yara ke mutuwa a sanadiyar wannan cuta ta Kyanda wadda ya ce, za a iya riga-kafinta.

Dr. Ghebreysus ya kara da cewa, dole ne a tabbatar kowanne yaro ya amfana da riga-kafin cutar domin ceto rai.

Rahoton Hukumar Lafiyar ta Duniya ya ce, cutar Kyanda ta fi tasiri a yankin kasashen Afrika da ke Kudu da Sahara, inda da dama daga cikin kananan yara ke tsallake karbar riga-kafin cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI