Jami'an tsaron Serbia sun yi barazanar garkame dan wasan Real Madrid
Wallafawa ranar:
Jami’an tsaron Serbia sun yi gargadi dan wasan gaba na Real Madrid Luka Jovic da cewa za su iya garkame shi gidan Yari a kowane lokaci daga yanzu, muddin yaki bin umarnin killace kansa daga jama’a a kasar saboda annobar Coronavirus.
Jovic yayi tattaki zuwa gida Serbia ne bayan dakatar da dukkanin matakan gasar kwallon kafar Spain.
A baya bayan nan ne dai aka ga matashin dan wasan yana yawatawa a titunan babban birnin kasar Belgrade, duk da cewa gwamnati ta umarci duk wani bako ko dan kasar da ya koma gida daga kasashen da annobar murar ta Coronavirus ta shafa da ya killace kansa tsawon kwanaki 28.
Wannan ce at sanya ma’aikatar cikin gidan kasar ta Serbia gargadin cewar tana iya iza keyar duk wanda ya sabawa umarnin killace kai zuwa magarkama, komai shahararsa ko arzikinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu