Wasanni-Coronavirus

Annobar coronavirus ta tilasta dage gasar Olympics ta bana

Hukumar gudanar da gasar Olympics ta duniya ta sanar da dage gasar da aka shiya gudanarwa a Japan na wannan shekara sakamakon cutar coronavirus, inda ta sanya shekarar 2021 a matsayin lokacin da za’a gudanar da gasar.

Japan ce dai ke shirin karbar bakoncin gasar ta Olympics wadda aka tsara gudanarwa a watan Yulin shekarar nan.
Japan ce dai ke shirin karbar bakoncin gasar ta Olympics wadda aka tsara gudanarwa a watan Yulin shekarar nan. AFP/Kazuhiro Nogi
Talla

Bayan tattaunawar da akayi ta waya tsakanin shugaban hukumar wasannin na Olympics Thomas Bach da Firaministan Japan Shinzo Abe, bangarorin biyu sun amince da daukar wannan mataki.

Firaminsta Abe ya ce Bach ya amince da bukatar da ya gabatar masa na dage wasannin daga bana zuwa badi, sakamakon matsin lamba daga wasu kasashe wadanda suka fara bayyana janyewa daga gasar baki daya.

Sanarwar hadin gwuiwar da Bach da Abe suka gabatar, ta ce Japan za ta cigaba da rike wutar gasar na Olympics har zuwa badi.

Tun daga shekarar 1948 ba’a taba samun lokacin da aka kasa gudanar da gasar ba kowanne shekaru 4 sai wannan karo da cutar coronavirus ta hana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI