Faransa

Faransa ta gargadi ‘yan kasar kan shan ruwan sabulu don maganin coronavirus

Wani shagon sayarda magunguna a birnin Paris. 24/3/2020.
Wani shagon sayarda magunguna a birnin Paris. 24/3/2020. AFP / Alain Jocard

Hukumar kula da magunguna a Faransa ta gargadi al’ummar kasar da kada su kuskura su yi amfani da shawarar shugaban Amurka Donald Trump wajen amfani da Chloroquine, ko kuma dirkawa cikinsu sabulun wanke hannaye a matsayin maganin coronavirus.

Talla

Hukumar tace daga cikin mutane 321 da aka samu sun sha irin wadannan magunguna na shugaba Trump, kusan rabinsu Chloroquine suka sha ba tare da shawarar likita ba.

Ita ma kungiyar kula da ayyukan likita na kasashen Turai tayi gargadi dangane da kwankwadar irin wadannan magungunan.

Ranar alhamis da ta gabata, jaridar Washington Post ta ruwaito shugaban Amurka Donald Trump na yiwa kwararru tayin bukatar duba yiwuwar amfani da sabulu ko sinadaran tsaftace muhalli wato disinfectants a Turance, wajen kashe kwayoyin cutar coronavirus a cikin jikin dan Adam, ta hanyar soma baiwa marasa lafiya suna sha bayan sarrafa sinadaran.

Sai dai tuni kwararrun suka bayyana tunanin a matsayin “ganganci” domin kuwa sinadaran na disinfectants dake kashe cutar coronavirus a matakin muhalli, mummunar guba ce ga jikin dan Adam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.