WHO-Coronavirus

Sabon bincike ya nuna coronavirus na iya yaduwa ta iska- WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce akwai shaidun da ke nuna cewar ana iya daukar cutar coronavirus ta iska, sakamakon binciken da wasu masana kimiyya suka yi, wanda ke nuna cewa kwayar cutar na iya tafiyar fiye da mita biyu kafin ta fadi.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus. Christopher Black/WHO
Talla

Farfesa Benedetta Allgranzi, jami’ar Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar da wannan sabon rahoto, inda ta ke cewa lalle sun tabbatar da wannan sabon bincike, saboda haka yana da muhimmanci mutane su fahimci wannan sabon matsayi domin kiyaye wa.

Binciken da masana kimiyar 239 suka yi a duniya, ya ce cutar na iya tafiyar fiye da mita biyu, lokacin da wanda ya harbu da ita ya numfasa ko kuma ya zubar da wani ruwa daga jikin sa.

Kafin dai wannan lokaci Hukumar ta ce ana yada wannan cutar ne sakamakon mu’amala tsakanin mai dauke da ita, abinda ya sa aka bukaci bayar da tazarar akalla mita biyu tsakanin jama’a wajen huldar yau da kullum.

Ya zuwa yanzu cutar ta kashe mutane dubu538 da 326 a fadin duniya, bayan ta kama mutane miliyan 11 da dubu 645 da 810, yayinda miliyan 6 da dubu 116 da 100 kuma suka warke.

A nahiyar Turai kawai cutar ta kashe mutane sama da dubu 200 yayinda ta kashe mutum dubu 139 da 38 a Amurka da Canada, sai kuma wasu dubu 11 da 672 a nahiyar Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI