WHO tace watakila baza a samu maganin korona ba

Ma'aikacin lafiya dake kula da masu dauke da annobar korona a kasar Habasha
Ma'aikacin lafiya dake kula da masu dauke da annobar korona a kasar Habasha Amanuel Sileshi / AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin cewa mai yiwuwa ba za’a taba samun maganin cutar Coronavirus ba duk da kokarin da kasashen duniya da kamfanoni ke  yi don lalubo maganin cutar. 

Talla

Wannan gargadi na zuwa ne a daidai lokacin da mutane da suka harbu suka zarce miliyan 18, yayinda mamata suka doshi dubu 690.

Hukumar WHO ta ce yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a duniya ya zarta miliyan 18, daga cikinsu kuma annobar ta lakume rayukan akalla mutane dubu 689 da 758, tun bayan bullarta daga China a watan Disambar shekarar bara.

Annobar ta yiwa Amurka ta’adi inda ta lakume rayukan mutane dubu 154 da 860, sai Brazil da ta rasa mutane dubu 94 da 104, a Mexico kuma mutane dubu 47 da 746 cutar ta halaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.