WHO-Coronavirus

WHO ta tara dala miliyan 700 don samar da maganin Coronavirus

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres tare da shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres tare da shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus. Salvatore Di Nolfi/Pool via REUTERS

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da tara kudin da yawansu ya kai dala miliyan 700, wanda ke matsayin kusan rabin kudin da ta ke fatan harhadawa don yakar annobar cutar coronavirus da kuma samar da magani ko allurai ga ilahirin kasashen duniya.

Talla

A cewar hukumar ta WHO ta bakin daraktan ta na Nahiyar Afrika, masu bayar da tallafi na kasashen duniya ne suka samar da kudaden dala miliyan 700, yana mai cewa duk da ya ke bai kai yawan kudin da hukumar ke nema ba, abin alfahari ne nasarar samun tattara adadin.

Shirin COVAX hukumar ta WHO na son hada dala biliyan 2 da za yi amfani da su wajen sayen maganin da nufin wadata kasashe da shi ba tare da fifita ma’azurta akan matalauta ba.

A cewar Matshidiso Moeti daraktan na WHO a Afrika yanzu haka kasashen Afrika ciki har da Afrika ta kudu da Gabon da Namibia da kuma Equatorial Guinea sun aminta da bayar da kaso mai tsoka doga shirin na COVAX don samar da maganin cutar ta COVID-19.

Shirin na COVAX dai hadaka ne tsakanin katafaren kamfanin harhada magunguna na GAVI da WHO da kuma CEPI wanda zai samar da magungunan biliyan 2 don wadata duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.