Sanakara

Macron ya bukaci mata su rika gwajin sankarar mama

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron (Ludovic Marin / POOL via AP)

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci mata da su ci gaba da yin gwajin k cutar sankarar mama domin sanin halin da suke ciki a kodayaushe.

Talla

A sakon da ya aike wa matan Faransa a karshen mako, shugaba Macron yace duk da yake a yau duniya na fafutukar yaki da annobar korona wadda ke ci gaba da dibar rayuka, wannan ba zai hana matan zuwa yin gwaji domin sanin halin da suke ciki ba.

Macron ya ce ya san har yanzu akwai matan da ba sa iya zuwa asibiti sakamakon fargabar wannan cuta ta korona, amma zuwa yin gwajin na da matukar tasiri.

Shugaban ya ce mace guda daga cikin mata 8 na fuskantar kamuwa da wannan cuta, wadda gano ta da wuri kan taimaka wajen yin maganinta da kuma ceto rayuka.

Macron ya yaba wa masu wayar da kan jama’a wajen ganin matan sun rungumi tsarin yin gwaji akai-akai domin sanin halin da suke ciki a kodayaushe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.