Lafiya

Interpol ta kwace rigakafin coronavirus na bogi

Hukumar Interpol ta gargadi kasashen duniya kan samar da rigakafin coronavirus na bogi.
Hukumar Interpol ta gargadi kasashen duniya kan samar da rigakafin coronavirus na bogi. Luis ROBAYO AFP/File

Jami’an ‘yan sandan China da na Afrika ta Kudu sun kwace dubban rigakafin coronavirus na bogi kamar yadda Hukumar ‘Yan Sandan Kasa da Kasa ta sanar. 

Talla

Hukumar ‘Yan Sandan Kasa da Kasa ta Interpol mai shalkwaata a birnin Lyon ta ce, an gano akwatina 400 masu dauke da kwatankwacin alluran rigakafin coronavirus na bogi har  guda  dubu 2 da 400 da aka jibge a dakin adana kayayyaki na Germiston da ke wajen birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu.

Kazalika  jami’an tsaron sun kuma gano  takunkumai na bogi, sannan kuma suka kama wasu Sinawa da mutanen Zambia da aka samu cikin harkar.

A can kasar China kuwa, rundunar ‘yan sandan ta yi nasarar gano wani gungun miyagu mai sayar da alluran rogakafin Covid-19 na bogi a wani bincike da ta kaddamar wanda Hukumar Interpol ta dauki nauyi.

A samamen da ‘Yan sandan suka kai a Chinar, sun cafke mutane 80 tare da kwace  rigakafin na bogi fiye da dubu 3 da aka sarrafa a wata haramtacciyar farfajiya.

Tun a farkon wannan shekarar ce, Hukumar ‘Yan sandan Kasa da Kasa ta gargadi hukumomin  kasashen duniya cewa, su  daura damarar tunkarar  wani gungun miyagu da ke shirin samar da haramtaccen rigakafin coronavirus  a zahiri da kuma yanar gizo.                                                                  

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.