WHO-Suga

Mutum miliyan 422 na fama da ciwon Suga a sassan Duniya- WHO

Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus. AP - Salvatore Di Nolfi

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cutar suga a jerin cutukan da ke kisan sunkuru a tsakanin al’umma bayan karuwar mace-mace sanadiyyarta da akalla kashi 70 wanda ke nuna bukatar sake jajircewa a yaki da cutar dai dai lokacin da ake cika shekaru 100 da fara samar da sinadarin Insulin mai taimakawa wajen rage kaifinta.

Talla

WHO wadda ke bayyana nasarar da ake samu a wadata Duniya da sinadarin na insulin mai rage kaifin ciwon Suga, ta ce har yanzu akwai bukatar kara kaimi a yaki da cutar ta Diabetes ko suga, bayan matakin kaddamar da wani sabon shiri da zai magance yawan kamuwa da cutar da kuma bayar da kulawar da ta kamata ga masu fama da ita.

Shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce yanzu ne lokacin da ya kamata a dauki tsauraran matakan yaki da cutar baya ga bayar da kulawa bai daya ga masu fama da ita la’akari da irin yadda cutar ke kisan sunkuru.

A cewar Tedros Adhanom cikin shekaru 40 da suka gabata ana ci gaba da samun hauhawar sabbin kamuwa da ciwon suga lamarin da ke matsayin babban abin damuwar hukumar duk da kasancewar cutar ba mai yaduwa daga mutum zuwa mutum ba, amma tana ci gaba da kisan sunkuru ga wadanda ke fama da ita.

Hukumar ta WHO ta ce yanzu haka akwai mutum miliyan 422 masu fama da cutar ta suga a sassan Duniya galibinsu a kasashe matalauta yayinda ake samun mutuwar akalla mutum miliyan 1 da dubu 6 a kowacce shekara baya ga sabbin kamuwa fiye da miliyan 2 alkaluman da ke mayar da cutar ta 9 a jerin cutuka mafiya hadari da ke kisan jama’a.

WHO wadda ke jagorantar bikin cika shekaru 100 da samar da sinadarin insulin wanda manyan kamfanonin Duniya 3 ke kan gaba wajen fitarwa, ta ce abin takaici ne yadda alkaluman mutanen da ke fama da cutar ke karuwa maimakon raguwa, wanda ya tilasta samar da sabon tsarin da nufin bayar da kulawa ta musamman ga masu dauke da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.