Coronavirus-Rigakafi

Daskarewar jini ta allurar Johnson ba ta da illa-EU

Samfurin rigakafin Jonhson and Johnson
Samfurin rigakafin Jonhson and Johnson AP - Mary Altaffer

Hukumar Kula da Ingancin Magunguna ta Turai ta ce daskarewar jinin da ake samu sakamakon amfani da allurar rigakafin korona ta Johnson and Johnson, ba ta da illar da za a daina amfani da ita.

Talla

Sanarwar da hukumar ta bayar sakamakon korafin da ya biyo bayan matsalar da wasu da aka yi wa allurar suka fuskanta, ta ce alfanun da ke tattare da maganin sun zarce matsalar da ake samu.

Maganin Johnson and Johnson shi ne na biyu da aka danganta da samun daskarewar jini daga mutanen da suka yi amfani da shi bayan Astrazaneca.

Shugabar Hukumar Emer Cooke ta ce, yawan mutanen da aka samu da matsalar ba su taka kara sun karya ba, lura da mutane sama da miliyan 7 da suka karbi allurar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.