Malaria ta fara raguwa a Afrika-Rahoto
Wallafawa ranar:
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce shekaru biyu bayan kaddamar da allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro, ta yi nasarar yi wa yara sama da 650,000 allurar a kasashen Kenya da Ghana da Malawi.
Rahotan yaki da cutar Malaria na shekarar 2020 da hukumar ta gabatar, ya bayyana raguwar cutar musamman a kasashen Afrika da ake samun masu mutuwa sakamakon cutar.
Rahotan na shekara shekara ya bayyana cewa, an samu asarar rayukan mutane dubu 411 a shekarar 2018 sakamakon kamuwa da cutar Malaria, yayin da adadin mamatan ya kai 409,000 a shekarar 2019.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 90 na mutanen da suka mutu sakamakon cutar Malaria a Afirka, yara ne wadanda yawansu ya kai 265,000.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu