WHO-Malaria

WHO ta sha alwashin kawar da zazzabin cizon sauro nan da 2025

Karkashin wani shiri da WHO ta kaddamar ta sanar da aniyar kakkabe cutar ta cizon sauro a kasashe 25.
Karkashin wani shiri da WHO ta kaddamar ta sanar da aniyar kakkabe cutar ta cizon sauro a kasashe 25. PHILIPPE HUGUEN AFP/File

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta kaddamar da wani yunkuri na kawar da cutar zazzabin cizon sauro daga doron kasa nan da shekarar 2025, yayin da ta ce za ta taimakawa kasashe 25 da ke fama da matsalar.

Talla

WHO ta jaddada cewar kawar da cutar wadda ke kashe mutane akalla dubu 400 a duniya duk shekara ya zama wajibi ga kowacce kasa.

Rahotan wanda ke zuwa kafin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauron da za a yi ranar lahadi mai zuwa, ya ce WHO ta yi nasarar taimakawa kasashe 21 wajen magance cutar a karkashin shirin da ta kaddamar a shekarar 2017, kuma 8 daga cikin su sun samu nasara da suka hada da China da Iran da kuma Paraguay.

Hukumar ta ce ta gano wasu gungun kasashe 25 da ke da kwarin gwuiwar kawar da cutar baki daya daga kasashen su nan da shekarar 2025 da suka hada da Guatemala da Honduras da Koriya ta Arewa da kuma Thailand wadanda ta ce za ta taimaka musu wajen samun nasara.

WHO ta ce wadannan kasashe za su karbi taimako na musamman da kuma kwarewar masana wajen ganin sun samu nasarar da suka saka a gaba.

Rahotan hukumar na watan Nuwambar bara ya ce akalla mutane miliyan 229 suka gamu da cutar da ke da nasaba da zazzabin cizon sauro a shekarar 2019, yayinda sama da kashi 90 na mutanen da ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro na fitowa ne daga Afirka, kuma sama da 265,000 daga cikin su yara ne kanana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.