WHO-Tedros

Tedros Adhanom na shirin neman karin wa'adin shugabancin WHO

Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Ghebreyesus yayin taron manema labarai a birnin Geneve.
Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Ghebreyesus yayin taron manema labarai a birnin Geneve. AP - Salvatore Di Nolfi

Rahotanni daga Geneva sun ce shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Gebreyesus zai nemi wa’adi na biyu a shugabancin hukumar domin aiwatar da manufofin da ta sanya a gaba.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya jiyo daga wasu majiyoyi da suka tabbatar masa da labarin cewar Tedros zai sake takara bayan karewar wa’adin sa a shekara mai zuwa.

Sai dai Hukumar Lafiyar ta ki cewa komai kan takarar Tedros, amma ta ce nan da watan Satumba za ta gabatar da sunayen masu sha’awar takarar shugabancin ta.

An dai zabi Tedros Gebreyesus ne a shekarar 2017 abinda ya bashi damar zama dan Afirka na farko da ya shugabanci hukumar.

Idan ya samu goyan bayan manyan kasashen duniya, toshon ministan lafiyar na kasar Habasha zai kwashe shekaru 10 ya na jagorancin hukumar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI