Coronavirus

Rashin daukar mataki ya kawo bullar korona - Masana

Ma'aikatar kiwon lafiya dake kula da masu dauke da tsananin cutar korona a sasashin gaggawa na wani asabiti dake kasar India
Ma'aikatar kiwon lafiya dake kula da masu dauke da tsananin cutar korona a sasashin gaggawa na wani asabiti dake kasar India REUTERS - DANISH SIDDIQUI

Ayarin wasu masana game da lafiyar bil’adama na wata kungiyar mai zaman kanta, sun gano cewa barnar da annobar cutar Coronavirus ta yi  da an dauki matakan da suka dace tun da farko da ba tayi barna sosai ba.

Talla

Masanan masu zaman kansu na cewa gurguwar shawarwari da aka yi ta dauka suka kai da rasa rayukan mutane miliyan 3.3 a sassan duniya, bayaga durkusar da tattalin arzikin kasashen duniya.

Kungiyar masanan mai suna Independent Panel for Pandemic Preparedness and response na ganin hukumomi sun gaza kare jama'a daga annobar coronavirus.

Masana sun gaza sanin musabbabin korona

Masanan sun fito fili suka ce tun bullar cutar daga birnin Wuhan na kasaar China a watan 12 na shekara ta 2019 lamarin babu sauki, kuma kasashen duniya sun gaza sanin na yi.

Domin magance halin da ake ciki yanzu, a cewar masanan ala tilas  manyan kasashen duniya masu hali, su taimakawa kasashen duniya marasa karfi, da magungunan da aka tanadar.

Kazalika masanan na son ganin attajiran kasashen duniya, sun tallafawa sabbin kungiyoyin agaji don tunkarar wata annobar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.