Lafiya-Kimiya

An gano hanyar maido da ganin makafi a duniya

Wata tawagar masu fama da larurar makanta
Wata tawagar masu fama da larurar makanta REUTERS - ENRIQUE MARCARIAN

A karon farko a tarihi, masana kimiya sun yi nasarar maido da ganin wani makaho ta hanyar sauya kwayoyin halittar idanunsa.

Talla

Masanan sun yi amfani da kimiyar dashen sinadarin Protein cikin kwayoyin halittar kwakwaluwar makahon don isar da haske cikin idanunsa, kimiyar da ta samo asali fiye da shekaru 20 da suka gabata.

A wasu lokuta, larurar makanta na tsananta ne saboda tauyewar sinadarin da ke isar da sakon haske cikin idanu daga kwakwaluwar dan adam kamar yadda kimiya ta ce.

Yanzu haka masana kimiyar na Turai da Amurka sun yi gwajin farko kan wani mutun wanda ya rasa ganinsa shekaru 40 da suka gabata a dalilin makantar gado, inda suka fara yi masa magani  ta hanyar shigar masa da sinadarai masu karbar haske a cikin kwakwaluwarsa.

Masanan sun tsikara allura cikin idanunsa tare da kwashe watanni wajen farfado da wani bangare na ganinsa ta hanyar makala masa tabarau na msamman  mai fitar da haske.

Farfesa Jose-Alain Sahel, daya daga cikin masanan da suka gudanar da binciken kan lamarin a jami’ar Sorbonne ta Faransa da kuma Cibiyar Binciken Cutuka, ya bayyana cewa, gwajin da suka yi na a matsayin wata manuniya cewa, za a iya maido da ganin wasu makafi a duniya.

Kodayake masanin ya ce, za a dauki dogon lokaci kafin fara yi wa makafin magani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.