WHO-Coronavirus

WHO ta amince da sahihancin nau'in rigakafin corona na China

Nau'in rigakafin Sinovac ba Rasha.
Nau'in rigakafin Sinovac ba Rasha. REUTERS - ATHIT PERAWONGMETHA

Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince da maganin rigakafin cutar coronar da kasar China ta samar da ake kira Sinovac wanda shi ne na biyu da kasar ta samar domin yaki da cutar.

Talla

Shugaban Hukumar Tedros Adhanom Gebreyesus ya bayyana farin cikin sa da matakin wanda ya biyo bayan amincewa da sahihancin sa bayan gwajin da kwararun hukumar suka yi.

Gebreyesus ya kuma bayyana cewar sabon maganin na Sinovac yana da saukin ajewa sabanin sauran magungunan da wasu kasashe suka samar.

A watan jiya Hukumar ta amince da maganin Sinopharm daga China domin amfani da shi wajen rigakafin cutar wadda tayi sanadiyar mutuwar mutane akalla sama da miliyan 3 da rabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.