WHO-Coronavirus

Manyan hukumomin Duniya na son samar da daidaito a yaki da corona

Wasu alluran rigakafin corona.
Wasu alluran rigakafin corona. AP - Rafiq Maqbool

Shugabannin manyan hukumomin duniya da suka hada da asusun bada lamuni na IMF, da hukumar lafiya ta duniya WHO da bankin duniya, da kuma hukumar kasuwancin ta WTO sun bukaci kasashe masu arziki su kara kaimi wajen daukar matakai da ware kudaden da za a yi amfani da su wajen gaggauta kawo karshen annobar corona.

Talla

Shugabannin manyan hukumomin na duniya 4 sun yi kiran ne yayin taron manema labarai na hadin gwiwar da suka yi a jiya Talata, inda suka bukaci kasashe kungiyar G7 mafiya karfin tattalin arziki da su tallafawa shirin asusun bada lamuni na IMF, da a karkashinsa zai samar da dala biliyan 50, kudaden da za a yi amfani da su wajen kawo karshen annobar corona ta hanyar daidaita rabon alluran rigakafin cutar tsakanin kasashe masu arziki da matalauta.

Yayin gabatar da shirin nasa a makon jiya, asusun bada lamunin na duniya IMF ya ce za a yi amfani da biliyoyin dalar wajen yiwa kashi 40 na yawan al’ummar duniya allurar rigakafin Korona zuwa karshen shekarar 2021 da muke, yayin da za a yiwa ragowar kashi 60 alurar a cikin shekarar 2022 mai kamawa.

Wannan sabon yunkuri na zuwa ne a yayin da kasashe masu arziki suka bar matalauta a baya wajen yiwa al’ummominsu allurar rigakafin Korona, yanayin da masana suka ce baiwa annobar damar cigaba da wanzuwa bayan lakume rayukan mutane fiye da miliyan 3 da rabi.

Sai dai hukumomin na IMF, WHO, WTO da kuma bankin duniya sun dora alhakin matsalar rashin daidaiton da aka samu tsakanin kasashen masu arziki da kuma matalauta akan bayyanar sabbin nau’ikan cutar Koronar musamman a kasashe masu tasowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI