China-Malaria

WHO ta wanke China daga jerin kasashe masu fama da Malaria

China ce kasa ta 40 a Duniya da ta yaki cutar Malaria.
China ce kasa ta 40 a Duniya da ta yaki cutar Malaria. Olympia DE MAISMONT AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da kawo karshen zazzabin cizon sauro a China, bayan tsawon shekaru saba’in da kasar ta dauka ta na kokarin kawar da cutar. Nasarar na zuwa bayan shafe shekaru 4 a jere ba atre da samun wanda yak amu da zazzabin na cizon sauro ba.

Talla

Nasarar kawo karshen cutar ya zo ne bayan dimbin shekarun da kasar ta dauka tana yaki da matsalar, wanda WHO ta ce hakan manuniya ce kan yadda za a iya kawar da wannan cuta daga doron kasa baki daya.

Kasashen da suka jera shekaru uku ba tare da samun bullar cutar ba, sukan mika bukatar takardar shaida daga WHO game da halin da ake ciki kan zazzabin na Malaria, amma dole ne su gabatar da kwararan hujjoji da matakan da suka dauka na dakile sake bullar cutar.

China ta kasance kasa ta 40 da WHO ta tabbatar da rashin cutar ta Malaria, bayan kasashen Paraguay da Uzbekistan wadanda WHO ta bayyana a matsayin wadanda suka kawo karshen cutar a 2018, sai Algeria da Argentina a 2019, da kuma El Salvador a 2021.

Rahoton WHO na Duniya kan zazzabin Malaria na 2020 ya yi gargadi game da yadda cutar ke kara bazuwa, musamman a kasashen Afirka da cutar tafi kamari wanda hakan ke janyo mace-mace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.