Lafiya-Tarin fuka

Shekaru 100 da kirkirar rigakafin tarin fuka a duniya

Wani likita yayin nazari kan hoton kirjin wani mai fama da cutar tarin fuka ko TB a asibitin dake yankin Gugulethu na birnin Cape Town a Afrika ta Kudu. 9/11/2007.
Wani likita yayin nazari kan hoton kirjin wani mai fama da cutar tarin fuka ko TB a asibitin dake yankin Gugulethu na birnin Cape Town a Afrika ta Kudu. 9/11/2007. AP - Karin Schermbrucker

Yayin da aka cika shekaru 100 da gano allurar kariya daga tarin fuka a duniya wato BCG, to sai dai masu fafutukar ganin an kawo karshen wannan cuta, sun bukaci a samar da wata sabuwar allurar rigakafi mai karko nan zuwa 2025.

Talla

Kwararru da kuma wakilan kungiyoyin da ke kokawor ganin an kawo karshen wannan cuta ta tarin TB, sun ce akwai bukatar kara yawan kudaden da ake warewa don gano sabon maganin warkar da ita.

A cewarsu, duka duka Dalar Amurka milyan 117 ne aka ware wajen gudanar da binciken gano sabon maganin cutar tun 2019, a maimakon Dala milyan 550 da ake bukata kowace shekara matukar dai ana son cimma burin da aka sanya a gaba kafin 2025.

Masu wannan gwagwarmaya sun bayar da misali da yadda kasashen duniya suka ware Dala bilyan 100 a cikin shekarar da ta gabata don samar da allurar rigakafin korona kamar dai yadda Dakta Lucica Ditiu shugabar cibiyar da ke yaki da wannan tari na TB a duniya ta sanar.

Yanzu haka dai cutar TB na kashe mutane akalla dubu 4 a kowace rana ta Allah, duk da cewa allurar BCG da ake amfani da ita na bayar da kariya ga 60% zuwa 80% na yaran da aka yi wa ita a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.