Faransa-Coronavirus

Faransawa miliyan 40 sun yi allurar korona

Kimanin mutane miliyan 40 sun karbi allurar rigakafin korona a Faransa
Kimanin mutane miliyan 40 sun karbi allurar rigakafin korona a Faransa AP - Alexander Zemlianichenko

Kawo yanzu adadin mutanen da aka yi wa allurar rigakafin korona ya kai miliyan 40 a Faransa, kamar dai yadda shugaban kasar Emmanuel Macron ya sanar.

Talla

Shugaba Macron ya ce daga cikin wannan adadin akwai wadanda aka yi  wa allurar sau biyu da kuma wadanda aka yi akalla sau daya, inda ya ce a cikin makonni biyu da suka gabata kawai an yi wa akalla miliyan 4 allurar.

Shugaban wanda ke zantawa da menama labarai daga tsibirin Polynesia inda yake gudanar da ziyarar aiki, ya ce wannan dai na nuni da cewa kawo yanzu 60% na al’ummar kasar ta Faransa ne aka suka karbi wannan rigakafi.

Sanarwar dai ta zo ne kwana daya bayan da ‘yan majalisar dokokin kasar suka amince da sabuwar dokar da ke tilasta wa mutane nuna katin shaidar cewa an yi masu wannan allura kafin samun damar shiga a gidajen cin abinci da sauran wurare na tarukan jama’a.

To sai dai sabuwar doka na shan suka daga wani rukuni na al’ummar kasar, yayin da shi kuma shugaba Macron ya bayyana irin wadannan mutane a matsayin wadanda ba san ciwon kansu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.