WHO-Malaria

WHO ta sahale fara amfani da rigakafin malaria samfurin RTS,S/AS01

Cutar Malaria na kashe yara dubu 400 kowacce shekara.
Cutar Malaria na kashe yara dubu 400 kowacce shekara. PHILIPPE HUGUEN AFP/File

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta amince da fara amfani da nau’in allurar rigakafin zazzabin Malaria samfurin RTS,S/AS01 nau’in allurar da ke matsayin irinsa na farko da hukumar ta amince da amfani da shi kan jama’a don yaki da cutar wadda kan kashe yara dubu 400 kowacce shekara.

Talla

Matakin na WHO na zuwa bayan gwajin alluran rigakafin na Malaria ko kuma zazzabin cizon sauro har fiye da miliyan 2 a kasashen Ghana Kenya da kuma Malawi cikin shekarar 2019 nau’in allurar da kamfanin GSK ya samar tun a shekarar 1987.

A cewar shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanom Gebreyesus bayan gwajin kan kasashen 3 sakamakon na nuna cikin kwarin gwiwa za a iya amfani da shi kan jama’a a sassan Duniya don yaki da cutar wadda kan kashe kananan yara dubu 400 kowacce shekara galibi a kasashen Afrika.

Sanarwar da WHO ta fitar ta ruwaito Pedro Alonso daraktan shirin yaki da Malaria na hukumar na cewa matakin babban ci gaba ne a yaki da cutar da kan kashe yaro guda duk bayan mintuna biyu.

Wannan ne karon farko da WHO ta bayar da shawarar amfani da wata nau’in allurar rigakafi don yakar cutar ta Malaria da sauro ke yadawa.

Cutar ta Malaria da sauro ke yadawa na jerin cutuka mafiya kisa yanzu haka a Duniya, inda tafi kamari a kasashen Afrika da gabashin nahiyar Asiya.

Acewar Dr Pedro Alonso, bayan matakin WHO na sahale fara amfani da nau’in rigakafin cutar Malariyan samfurin RTS,S/AS01abin da ya rage shi ne samar da kudaden wadata kasashe da alluran don yaki da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI