Najeriya

An Wanke Nuhu Ribadu

RFI Hausa

Babban Mai gabatar da kara na Gwamnatin Najeriya, Mai sharia Mohammed Adoke ya janye jerin zarge-zarge da ake yiwa Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da masu karya tattalin arzikin kasar Nuhu Ribadu.A yanzu kenan an wanke Nuhu Ribadu daga tarin laifuffukan da suke zarginsa da aikatawa na kin bada bayanan kaddarorinsa ga Hukumar Kula da da’an Maaikata, ICPC.Nuhu Ribadu ya sha karyata zargin da ake yi masa.Cikin wadan da suka halarci zaman kotun ayau sun hada da tsohon Ministan Abuja Nasir El-Rufai wanda karshen makon daya gabata ne ya koma Najeriya daga gudun hijiraFemi Falana, Lauyan Nuhu Ribadu yaki fadawa manema labarai ranar da tsohon Shugaban Hukumar Yaki da masu karya tattalin arzikin Najeriya zai koma gida.